HUKUNCIN AUREN KISAN WUTA
AMBAYA TA 153 ****************** Assalamu alaikum Minene hukuncin Auren Dibar wuta a Musulunci? Shin hukuncin Yana da bambanci idan Macce ce ta shirya Auren Dibar wutar ba tareda sanin tsohon Mijinta ba? Minene hukuncin idan matar da Mijin suka shirya Auren Dibar wutar? Sannan hukuncin yana da bambanci idan sabon mijin da Aka Aura yana da Masaniya akan Auren Dibar wuta ne za ayi dashi? (daga Barrister Isma'il) AMSA ****** Wa alaikumus salam wa rahmatulLah. Wannan tambayar mun riga mun amsa irinta achan baya. Amma saboda muhimmancin Mas'alar, da kuma yawan faruwarka acikin al'ummah, sai naga cewa ya zama wajibi mu sake amsa wannan dinma. Imamuz-Zahabiy (rah) ya fada acikin shahararren littafinsa mai suna "KITABUL-KABA'IR" akan shafi na 141, Laifi na 53, yana cewa: Hadisi ya inganta daga Sayyiduna Abdullahi bn Mas'ud (ra) yana cewa: "MANZON ALLAH ﷺ YA TSINEWA MAI AUREN KISAN WUTA, DA KUMA WANDA AKAYI AUREN KISAN WUTAN DOMINSA". Imam Tirmidhy (rah) ...